2023: Yankin Kudancin Najeriya ne yakamata ya fitar da Shugaban Kasa -Ganduje

0
99

A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke kara karatowa, gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce Kudancin Najeriya yakamata a mikawa mulkin shugabancin Najeriya.

Ganduje ya yi bayanin hakan ne a Kano yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channel wanda aka sanya a yau Juma’a.

Yayin da aka tambaye shi kan shin daga wane yanki shugaban kasa zaj fito a 2023 sai ya ce “Yankin kudancin Najeriya amma akwai tattaunawar sulhu tsakanin mambobi.

” Tsarin karba-karba duk da baya cikin kundin tsarin mulkin kasar Najeriya, sai dai tsari ne na samun nasarar zabe”.

Yayin da aka tambaye shi kan ko jam’iyyar APC ta kyautatawa yan Najeriya tun da hau karagar mulki a shekarar 2015, gwamnan sai ya bayar da amsa cikin tabbatarwa.

Ya ce jam’iyyar APC karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta inganta tsaro tare da bunkasa tattalin arziki.

Ganduje ya kuma nuna cewa jam’iyyar nada karfin gwiwar lashe zaben shekarar 2023.

“Ina tunanin a shekarar 2023, APC za ta lashe zabe saboda mutane da dama suna shigowa jam’iyyar. Duk da mun rasa wasu gwamnonin sakamakon wasu matsaloli, a dai-dai lokacin wasu ke shigowa jam’iyyar”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here