2023: ‘Ku Ajiye Makamanku Akwai Lokacin Amfaninsu’, Sakon Abdullahi Abbas Ga Ƴan Daba

0
254

Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas ya kara ingiza magoya bayan jam’iyyar APC kan su dauki matakan hukunta duk wanda ke shirin magudin zabe a shekarar 2023.

Abdullahi Abbas, wanda ke batu kan PDP Kwankwasiyya, ya fadawa daruruwan magoya bayan jam’iyyar APC a filin wasa na Kano Pillars dake Sabon gari a Kano yau Juma’a yayin rantsar da shugabannin kananan hukumomi 44, cewa “Ku kai hari tare da hukunta dukkan wanda kuka gani yana kokarin satar kuri’u yayin zaben dake tafe.”

Idan za’a iya tunawa dai ba wannan ne karon farko da shugaban Jam’iyyar ta APC ke ingiza magoya baya ba a yayin zabe, inda ko a lokacin fara sabunta rijistar mambobin jam’iyyar ya yi gargadin cewa zasu dau tsauraran matakai kan duk wanda ke adawa da jam’iyyar.

Haka kuma, a wani lokaci a shekarar 2020, Abdullahi Abbas an jiyo shi na fadin cewa, za su dauki mataki kan dukkan wanda yayi kokarin mai-maita abinda ya faru a zaben gwamnan jihar na shekarar 2019.

Ya ce “Ina Umartarku ku hukunta duk wanda kuka gani a bakin akwatu yana kokarin yin magudin zabe, hukunci na ne, ba abinda zai faru”.

Shugaban kwamitin rikon na jam’iyyar APC ya bukaci daruruwan magoya bayansa wadanda ke dauke da muggan makamai wadanda suka kewaye shi da su adana makamansu saboda shekarar 2023, inda ya ce ” Ku ajiye makamanku kusa da ku akwai lokacin amfaninsu na musamman”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here