Na Matsu Ranar Muƙabalata da Malamai ta zo – inji Sheikh Abduljabbar

0
245

Tawagar lauyoyin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sun ce wanda suke karewar a shirye yake ya yi mukabala da sauran malamai kamar yadda gwammatin jihar Kano ta nema, bayan ta dakatar da shi daga yin wa’azi, bisa zargin kalaman da za su haifar da rikici.

“Ina farin ciki sanar da ku cewa nayi magana da wanda nake karewa dangane da shirin mukabala da gwamnatin jiha ta shirya da sauran malamai a jihar, ya fada min cewa yana Allah-Allah ranar ta zo.

” Don haka, ina tabbatar maka cewa Shekh Abduljabbar Nasir Kabara ya kintsa sosai kuma zai shiga tattaunawar ko da ba gwamnatin jiha ce ta shirya ba”, inji Barista Rabiu Abdullahi-Shuaibu yayin da yakewa manema labarai jawabi a Kano ranar Laraba.

A wata sanarwa da yafitar ranar 3 ga watan Fabarairu, Kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammadu Garba y sanar da dakatar da Abduljabbar daga yin wa’azi a jihar saboda gwamnati na zargin kalamansa na tada rikici ne.

Gwamnatin ta kuma bada umarnin rufe inda malamin ke karatu.

Yayin da yake mayar da martani kan matakin gwamnatin, Barista Abdullahi Shuaibu ya ce “Matakin da gwamnati ta dauka na dakatar da Abduljabbar daga wa’azi ya saba da doka, kamata yayi a bashi damar jin ta bakinsa kafin a yanke hukuncin”.

“A karar da muka shigar gaban babbar kotun tarayya a Kano mun nemi kotun ta bada umarnin janye jami’an tsaron daga gidan Shekih Abduljabbar, Masallacinsa da sauran wuraren tare da dakatar dasu daga zuwa wajen nan gaba.

“Mun nemi hakkin fadin albarkacin baki, da yin addini, an daga karar zuwa 18 ga watan Fabarairu”, inji Lauyan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here