“Nayi Farin ciki da Gwamnatin Tarayya ta bawa Jami’ar Maryam Abacha Lasisi” – Farfesa Adamu Gwarzo

0
191

Shugaba kuma Wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha(MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya yabawa gwamnatin tarayya da duk wadanda suka tallafa wajen bawa jami’ar lasisin fara karatu.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya yi yabon ne a ranar Laraba a sanarwar da ya fitar mai dauke da sa hannunsa kuma aka rabawa manema labarai.

Idan za’a iya tunawa dai a yan kwanakin nan gwamnatin tarayya ta bada lasisin fara aiki ga jami’o’i 20 masu zaman kansu ciki har da jami’ar Maryam Abacha.

Ya ce bada lasisin ya sanya shi farin ciki da kuma tabbatar da kudurinsa na ganin yan Najeriya musamman matasa sun samu ilimi wanda za’a kwatanta shi da irin na kasashen turai wanda hakan zai sa su dinga gogayya da sauran daliban jami’o’i a duniya.

Sannan ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Majalisar zartarwa ta kasa, da hukumar kula da jami’o’i ta kasa da sauran masu fatan alkhairi wadanda suka kirashi da masu turo sakon taya murna bisa samun lasisin jami’ar.

Farfesa Abubakar Gwarzo ya kara da cewa lasisin da gwamnatin tarayya ta bawa jami’ar zai bashi kwarin gwiwa wajen ci gaba da ayyukan ginin wasu tsangayoyi da sashin karatu a matsugunin jami’ar dake gari Gwarzo.

Ya bada tabbacin cewa, jami’ar zata yi duk mai yuwuwa wajen samar da dalibai na kwarai.

“Abin farin cikinmu ne ace mun ceto Jihar Kano, Najeriya da Afrika daga karancin jami’o’i”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here