Da a ce Donal Trump Ya Gayyaci Ganduje Da ya taimaka masa Wajen Murɗe Zaɓe – Inji Dan Majalisa

0
261

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado Doguwa, ya ce da ace tsohon shugaban kasar Amurka, Donal Trump ya nemi tallafin gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje da ba a kayar da shi a zaben kasar ba.

Alhassan Ado wanda ke wakiltar kananan hukumomin T/Wada da Doguwa a majalisar Wakilan Najeriya, a watan Nuwamba na shekarar 2019 yayi kurin yadda kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya amince a bashi sabbin motoci guda uku duk da umarnin kotu na soke zabensa.

Sai dai daga baya ya musanta bayanin nasa inda ya ce ba a fahimce shi bane.

A wani Bidiyo dake yawo a kafafen sadarwa na zamani an jiyo Dan majalisar na yiwa magoya bayansa bayanin karfin da gwamnan yake da shi wajen murdiyar zabe.

“Yayin da alamu suka fara nuna Trump zai sha kasa, da ya kirawo Ganduje a waya don ya tura masa Murtala Garo ko Alhassan Ado ko Kawu Sumaila ka Dan Majalisa Kabiru Rurum. Da labarin bai kasance yadda yake a yanzu ba.

” Gare mu Ganduje jami’ar Siyasa ne, yan siyasa za su shafe lokaci suna fada muku karya a kan lashe zaben 2023, suna fada muku shashanci ne”, inji Dan Majalisar.

Dayawan masu sanya ido a zabe sun yi zargin cewa jam’iyyar APC da hadin kan hukumar zabe da jami’an tsaro sun yi murdiya a zaben gwamnan jihar Kano na shekarar 2019.

A rahotan da ta fitar cibiyar bunkasa al’amuran dimukuradiyya CDD ta bayyana cewa kungiyoyin sa’ido a zaben sun ce an tafka magudi a zaben.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here