“Muna Son Yin Aure Amma Lefe na ci mana Tuwo a Kwarya” -Samari

0
440

Mahawara ta kaure a shafukan sadarwa na zamani kan kiraye-kirayen da wasu ke yi na a soke Kayan Lefe a Kasar Hausa yayin Bikin Aure.

Bayyanar wani bayani da ake alakanta shi da shehin Malami, Shekih Muhamad Bn Usman inda yake kira da a soke al’adar lefen ya kara zafafa muhawarar kan shin a soke lefen ko a barshi?.

A kan hakan ne jaridar PRIME TIME NEWS ta tattaro ra’ayoyin wasu samari da yan mata kan bukatar ta soke Kayan Lefe ko kuma barinta.

 

Sadiq Shehu Doguwa

“Wato a har kullum al’umar hauwasa kan sami wata mahanga guda daya su makale

Suyi ta kai kawo acikinta, yanzu dan kayan da zaka yi mata wanda zata ringa sakawa agidanka kana kani shi ne zai tsole maka idanu

Yanzu zakaso kanwarka akaita gidan miji da atamfa kala 2 da soson wanka da hijab 1 mayafi 1?, “.

 

Sadiq Hassan

“Ina son Aure Amma kuma babu Abun dake cimun tuwo A kwarya kamar lefe, Ina goyan bayan soke lefe dari bisa Dari”.

Najeeb Ibrahin Lawal

“Ni lefe zan mata, babu komai. Amman wallahi Sule bazan kashe akan party ba, sai dai ta fasa aure na”.

 

Ludufullahi

“Anawa ra’ayin bana goyan bayan a soke saidai adan sasauta saboda ko ta shigo gidan sai kaimata suttura”.

Malam Mubarak

“Shaikhul Islam Ibn taimiyyah yace a yayin da aure yayi tsada sai zina tayi araha____ lallai an kawo wasu al’adu dake kawo tsaiko ga samari da ‘yan mata wajan yin aure, an kallafawa samari yin kayan lefe baya ga fargabar gini ko Kuma kama haya… Uban amarya kuma an ko danginta an dora musu yin kayan daki…. Hakan tasa zina ke kara yawa a wannan al’umma tamu… Matasa mata da maza sun isa aure babu halin yi tun suna jurewa har takai ga sun fada barna… Ita fa sha’awa uwa tamkar yunwar ciki ce, wata fidira ce da Allah ya dora bayi akai….. Shawarata shine a saukakawa juna banda tsawwala koda za ayi wadancan abubuwan ya zamana an duba halin mutum in bashi da karfi yayi abinda ya sawwaka… Hakama dangin amarya suyi abubuwa gwargwadon halinsu kuma wadanda aka fi bukata kamar tukwane katifa da ‘yan tabarmi.

“A yayin da ku iyayen yarinya kuka saukaka masa wajan wadannan abubuwa ku sani kuma a daya hannun kuna da ‘ya’ya maza wadanda suma zasu ci moriyar wannan tsari a wani wajan .Wannan shine ra’ayina”.

 

Ahmad Sharif Sani

“A ra’ayina bana goyan bayan soke lefen sabida hakan zai sa samari su dinga Aure barkatai”.

Mustapha Sadisu Madugu

“Soke lefe ba shi ne mafuta ba saboda sau da yawa wasu mazajen basa iya yiwa iyalansu dinki bayan sun auresu, mafitar shine a sassautawa mazaje idan sun kawo adaina rainawa, ko yaya yake a karba ayi hakuri koda kuwa akwati shidace ko bakwai kada a raina koda ba a hada da gwala gwalaiba dayawa adaina rainawa.”

 

Khadija Abdullahi Habib

“Ba Wanda ya isa ya soke Lefe, dole maza su soke lefe”.

 

Yayin da wasu mazan ke goyan Bayan a soke lefan su ma wasu yan matan na kira a dena yin kayan daki.

 

Al’adar lefe dai ana yinta ne ta hanyar hada kayan sutura, kayan kwalliya da sauransu yayin da ake shirin Aure.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here