Ana Fama da Ƙarancin Ruwa a Jami’ar Bayero Kano Sakamakon Yajin Aikin Ma’aikatan Jami’o’i

0
175

Ana fama da matsalar karancin ruwan sha a Jami’ar Bayero Kano, biyo bayan yajin aikin da ma’aikatan Jami’o’i ke yi a fadin Najeriya.

Idan za’a iya tunawa dai a ranar Juma’a, 5 ga watan Fabarairu kungiyar SSANU da NASU, suka tsunduma yajin aiki bisa gazawar gwamnati na biya musu bukatunsu.

Wasu daga cikin bukatun kungiyoyin sun hada da yadda za’a tafikar da tsarin biyan Albashi na IPPIS, tsarin rabon alawus-alawus na Biliyan 40 da kuma mafi karancin kudin ariyas.

Binciken da jaridar Daily Nigerian ta yi yayi nuni da cewa matsalar karancin ruwa ta samu ne sakamakon rufe wajen ajiyar ruwa da kungiyar ma’aikatan Jami’a ke tafiyar dashi wadanda a yanzu haka suke yajin aiki.

Jaridar ta rawaito cewa, gidan wuta na Jami’ar yana rufe inda hakan ya sanya ajujuwa da gine-gine suke cikin duhu.

Wani dalibi da ya nemi a boye sunansa ya ce sakamakon rashin wutar lantarki, basa iya karatu a cikin dakin karatu ko kuma kusa da fitilar kan hanya.

“Muna shirin fara jarrabawa a kwanki kadan masu zuwa. Mun damu gaskiya.

” Motocin dake daukar dalibai daga tsohuwar jami’a zuwa sabon matsuguni suma an dakatar da su daga aiki saboda yajin aikin.

“Akwai bukatar a kawo karshen wannan yajin aikin. Gwamnatin tarayya yakamata ta kawo karshen wannan yajin aikin” inji dalibin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here