Allurar Rigakafin Korona na Mayar da Mutane Ƴan Luwaɗi da Maɗigo -Inji Wani Malami a Ƙasar Iran

0
195

Ayatollah Abbas Tabrizian wani shehin Malami a kasar Iran ya ce allurar riagakafin Korona na mayar da mutane yan Luwadi.

Jaridar The Jerusalem ta ambato malamin na ikirarin hakan ne a shafinsa na Telegram inda yake da mabiya 210, 000.

Kodayake bai bayyana wata sheda da za ta tabbatar da ikirarin nasa ba.

“Kar ku kusanci wadanda aka yiwa Allurar rigakafin Korona. Sun zama masu auren jinsi”, inji malamin.

Malamin yasha sukar irin magunguna da rigakafi wanda kasashen turai ke samarwa.

Sai dai ikirarin nasa kan rigakafin Koronar ya jawo masa suka daga mutane inda suke zargin sa da yunkurin hana yiwa mutane rigakafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here