Makarantar Hidayatul Adfal Ila Dinil Islam Wajila ta Gudanar da Bikin Saukar Al’Qur’ani Karo na 3

0
147

Makarantar MADARASATUL HIDAYATUL ADFAL ILA DINIL ISLAM WAJILA BANGAREN TAJWEED Dake Unguwar Dan Agundi ta gudanar da bikin Saukar Al’Qur’ani mai girma na dalibai 70.

Taron saukar wanda aka gudanar da shi a ranar Asabar ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban .

Yayin da yake zantawa da Jaridar PRIME TIME NEWS, Jagoran makarantar, Malam Muhammad Rabi’u Shu’aibu ya bayyana farin cikinsa bisa yadda makarantar ta yaye dalibai da suka kammala Sauka tare haddar Al’Qur’ani mai girma.

“Wannan Sauka da mu ke yi karo na uku ne, Saukarmu ta farko akwai dalibai guda 164 wadanda suka yi sauka kuma a karo na biyu mun yi sauka da dalibai 96 sannan a wannnan karo na uku dalibai guda 70, to idan ka hada da sanda muka fara yi zuwa yanzu, akwai dalibai guda 330 wadanda suka samu sauka a wannan makaranta banda kuma hafizai na Qur’ani da muka yaye a wannan makaranta”.

Shima daya daga cikin daliban makarantar da suka samu Sauke Al’qur’ani mai girma, Adnan Dahiru Lawan ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan rana.

“Muna Kara godewa Allah da ya kawo mu wannan rana da muka sauke Al’qur’ani mai girma”.

Sananan Dalibin ya shawarci yan uwansa dalibai da su ci gaba da zuwa makarantar tare da riko da littafin Allah mai tsarki.

Tun da farko dai shugaban makarantar, Malam Ado Abdu Gwangwazo ya gabatar da jawabin maraba da kuma tarihin makarantar.

Manyan bakin da suka halarci bikin saukar sun hada da, Manajan darakta na hukumar KAROTA, Dr. Baffa Babba Dan agundi, Shekh Shehu Uba Sharada, Alhaji Aminu Ibrahim Dutse, Dakta Akilu Sani Indabawa,Alhaji Mu’awiiya Abbas Sanusi Dan Makwayon Bichi da Shugaban karamar hukumar Birnj, Alhaji Sabo Muhammad Dantata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here