Femi Fani-Kayode Na Shirin Ficewa daga PDP zuwa APC

0
104

Wasu bayanai sun bayyana cewa, tsohon ministan harkokin sufuri na kasa, Femi Fani-Kayode zai fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC nan bada jimawa ba.

Wasu majiyoyi daga PDP da APC  sun bayyanawa jaridar Daily Trust a yau Litinin cewa, tsohon ministan ya yanke shawarar sauya jam’iyya daga PDP zuwa APC.

Majiyar ta labarta cewa, tsohon ministan na tuntubar masu ruwa da tsaki cikin jam’iyyar APC don shirin sauya shekar tasa.

Wata majiya mai tushe a shelkwatar APC ta kasa, ta shaidawa jaridar cewa, Fani-Kayode ya tattauna da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, don shirya sauya shekartasa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, tattaunawarsa da gwamna Yahaya Bello ta share fagen tattaunawa tsakaninsa da gwamna mai mala Buni kuma shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here