Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Yabawa Ganduje Bisa Matakan da Ya Dauka Kan Abduljabbar

0
177

Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya yabawa gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa matakan da ya dauka kan dakatar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara daga yin wa’azi a jihar Kano.

Idan dai za’a iya tunawa dai a ranar Laraba ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da dakatar da Malam Abduljabbar daga yin wa’azi tare da rufe masallacinsa nan take.

A karatun da tsohon Sarkin ke gudanarwa a duk ranar Lahadi daga jami’ar Oxford ta kasar Ingila, ya ya bawa malaman Kano da gwamnatin Jihar Kano kan matakan da suka dauka.

“Jama’ar Kano a ci gaba da tsayawa, mu Kano mu tsaya kan Cewa mu Kano baza mu tsaya kan komai ba sai a kan akidar da shehu Usman Dan Fodio ya dora mu akai akidarmu ta Ahalissuna Wal-jama’a.

“Wannan matakai da gwamnati da gwamna ya dauka abu ne da yakamata a yaba masa.”

Tuni dai gwamnatin Kano ta sanar da cewa zata shirya wani zaman keke da keke tsakanin malaman Kano da Abduljabbar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here