Ƴan Matan Dake Tallan Fura da Nono ne Ke Safarar Kwayoyi ga Ƴan Bindiga – Tambuwal

0
117

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya yi zargin cewa, yan matan dake siyar da Fura da Nono na safarar miyagun kwayoyi ga yan bindiga.

Ya yi zargin ne yayin da yake karbar tawagar Sheikh Ahamd Gummi wacce ke kokarin sanya yan bindiga su ajiye makamansu a ranar Asbaar a jihar Sokoto.

“Wani abokin aikina, gwamna mai ci a yanzu ya taba bani labarin wani lamari da ya faru. Ya fadamin cewa ya taba ziyartar wata riga don bunkasa kasuwancin mata dake zuwa kasuwanni suna kawo fura da nono .

” Yayin da na neme su, daya daga cikinsu sai ta gudu. Ya tambaya mene ne matsalar sai aka fada masa cewa, ba nono da fura take daukowa a kwarya ba, sai dai kwayoyi take daukowa.

“Gwamnan ya yi min bayani sosai kan kwayar da yan bindiga ke amfani da ita.

” Saboda haka, dole ne muyi aiki don magance safarar miyagun kwayoyi. Idan kuwa ba haka ba, zamu kashe miji ne bamu sare kansa ba”, inji shi.

Gwamnan ya yi bayanin cewa, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya.

Tawagar ta Sheikh Gummi ta kuma ziyarci fadar Sarkin Musulmai, Muhamamd Sa’ad Abubakar a fadarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here