Kotu ta Bada Umarnin Rufe Masallacin Abduljabbar Nan take tare da Dakatar da shi daga yin Wa’azi

0
96

Kotun Majistiri a Kano ta bada umarnin rufe masallacin Abduljabbar Nasiru Kabara tare da dakatar da malamin daga yin wa’azi.

Mai shari’a Mohammed Jibrin a jiya Alhamis ya ce umarnin kotun na zuwa ne bayan bukatar da lauyan mai kara, Barista Wada A Wada daga ofishin Antoni Janar na Kano ya shigar.

Kotun ta bada umarnin rufe masallaci da cibiyar Abduljabbar Nasiru Kabara dake Filin Mushe nan take har zuwa kammala binciken jami’an tsaro.

Sannan ta umarci Abduljabbar Nasiru Kabafa da ya dakata da yin wa’azi tare da kiyaye kalaman da za su haifar da rikici.

Sannan kotun ta umarci kafafen yada labarai da su dena sanya karatun malamin har zuwa lokacin kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here