Jami’an Tsaro Sun yiwa Gidan Shekh Abduljabbar Kawanya Don tabbatar da bin Umarnin Gwamnati

0
118

An hango jami’an tsaro da dama a kusa da gidan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara dake unguwar Gwale cikin birnin Kano.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, a safiyar ranar Alhamis ne gwamnatin Kano ta sanar da dakatar da shahararen malamin addinin musuluncin daga yin wa’azi a jihar bisa salon yadda yake koyarwa kan iya haifar da rikici.

Gwammatin jihar ta kuma umarci rufe dukkan inda malamin ke yin karatu har zuwa lokacin da jami’an tsaro zasu kammala bincike.

Jaridar ta Daily Trust ta rawaito cewa, motocin yan sanda biyar ne dauke da jami’an tsaro da suka hada da na farin kaya(DSS), da na Civil Defense suka yiwa gidan malamin kawanya don tabbatar da bin umarnin gwamnatin.

Kodayake basu dakatar da mabiya da masu jaje zuwa shiga gidan ba.

An ga daruruwan mabiyan malamin a kusa da gidansa da masallacin don jimami kan umarnin gwamnatin.

Sheikh Abduljabbar wanda mabiyin darikar Kadiriyya ne, ya na ta shan suka daga malamai da dama a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here