Cutar Korona ta Kashe Hakimi a Kano

0
98

Tsohon dan majalisar wakilai kuma tsohon mai baiwa gwamna Shekarau shawara kan fannin tattalin arziki, Dr. Abdullahi Maikano, ya rasu sakamakon cutar Korona.

Mai shekaru 72, kuma likitan dabbobi ya rasu ne a cibiyar killace masu dauke da cutar Korona ta Kwanar Dawaki inda yake karbar kulawa.

Ya rasu ya bar mata daya, ‘ya’ya da jikoki.

Yayin da yake tabbatar da rasuwar tasa, Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda yake makusanci da mamacin ya ce marigayin shi ne tsohon shugaban bankin kasuwanci na Kano kuma tsohon dan majalisar wakilar a jamhuriyar ta biyu.

Har zuwa rasuwarsa, shi ne Dallatun Bichi kuma hakimin Dawakin Tofa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here