A Bawa Kowanne Dan Najeriya Damar Mallakar Bindigar AK47 Don Kare Kansa – Gwamnan Taraba

0
101

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya bukaci gwammatin tarayya ta kyale yan Najeriya su mallaki bindigogi don kare kansu a dai-dai lokacin da ake fama da matsalar tsaro.

Gwamnan ya yi bayanin hakan ne a  jiya Talata yayin da shugabannin kananan hukumomi 15 na jihar suka kaimasa ziyarar ta’aziyyar daya daga cikinsu da yan bindiga suka sace tare kashe shi.

Ya koka kan tabarbarewar fannin tsaro inda ya ce lamarin yayi muni sosai.

“Lamarin tsaro a kasarnan yayi muni yakamata mu farka. Mu shugabanni ana ta bamu shawara don sauya tasiwirar tsaro, bazai yuwu ba kayi ta yin abu daya kuma ka tsammaci samun sakamako mai kyau”, inji shi.

“Idan baza mu iya samar da tsaro ga yan kasa ba, toh mu bawa kowa damar siyan bindigar AK47, saboda idan aka bawa kowa damar rike bindigar AK47, na rantse ba wanda zai zo gidanka”.

Gwamna Ishaku ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa ransu ta sanadiyar rashin tsaro, inda yayi bayanin cewa, marigayi Salihu Dovo shugaban karamar hukumar Ardo-Kola ya shirya taron samar da zaman lafiya da masu ruwa da tsaki kafin a kashe shi.

Ya yi bayanin cewa yayin da yan bindigar suka sace mamacin ya gane wasu daga cikinsu tare da kiran sunan daya wanda hakan ne yasa suka kashe shi.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, an kama mutane 4 inda ya bukaci jam’an tsaro su kamo duk wadanda ke da hannu a lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here