Za mu Sake Rufe Makarantu a Kasarnan Idan Har…… -Kwamitin Yaki da Korona

0
139

Kwamitin yaki da cutar Korona na fadar shugaban kasa ya ce ba zai dakata da rufe makarantu a kasarnan ba idan har aka ci gaba da samun yawaitar masu kamuwa da cutar Korona.

Jami’i a kwamitin na Yaki da Korona, Mukhtar Muhammed, ne yayi bayanin haka a wani Bidiyo da kwamitin ya wallafa a shafin Twitter ranar Litinin.

Ya ce, “Dangane da batun sake bude makarantu, abune da kwamitin yaki da Korona ya tattauna sosai da sosai. Ma’aikatar Ilimi ta yanke shawarar bude makarantu. Bisa fahimtarmu, jihohi ne ke son makarantu su kasance a bude.

“A yanzu kwamitin yaki da Korona na lura da hakan, muna kallon abinda ke tafiya, idan muka samu cewa ana ci gaba da samun yawaitar masu kamuwa da cutar da kuma samun hakan a makarantu, ba makuwa zamu rufe makarantun.

” Da farko, yakamata ace mun saurara bude makarantu amma yanzu makarantu sun kasance a bude, kwamitin yaki da Korona zai ci gaba da lura tare da aiki da makarantu don tabbatar da sun samar da matakan kariya tare da sanya mutane su bi matakan”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here