Sunday Igboho Ya Jagoranci Matasan Yarabawa Wajen Ƙone Gidajen Fulani a Jihar Ogun

0
238

Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya kara kone gidajen Fulani dake Igua yankin Arewacin Yewa a jihar Ogun.

Shugaban kungiyar Miyatti Allah reshen jihar Ogun, Alhaji Abubakar Ibrahim Dande ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, matasa karkashin jagorancin Sunday Igboho sun cinna wuta a gidan Sarkin Fulani na Igua, Alhaji Adamu Oloru.

“Sun kone gidaje da na Sarkin Fulani, Alhaji Adamu Oluro, wanda ke Igua a yammacin jiya Litinin.

” Sun kuma cinna wuta a kasuwar dabbobi.

“Mun sanar da jami’an tsaro, ciki har da jami’an tsaron farin kaya na DSS, yayin da muke da masaniyar zai zo.

“Mun saurari bayani a Rediyo, mun kuma gane cewa gwamnatin jiha ce ta sauke shi.

” Mun rasa mai taimako, babu wani mutum da zai iya kare mu.

“Jama’armu da dama sun gudu zuwa cikin dazuka”, inji shi.

Alhaji Muhammadu Chede ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, an kashe wani makiyayi mai suna Danwake kuma an kone gawarsa.

” Muna Randa ta Abeokuta yanzu haka, muna shirye-shiryen samun gawarsa domin binne shi”, inji shi.

A gefe guda kuma kwamishinan yan sanda na jihar Ogun na tattaunawa da al’ummar yankin da abin ya shafa don wanzar da zaman lafiyar.

Sunday Igboho ya dira a birnin Abeokuta a ranar Litinin inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar Ogun ce ta gayyace shi.

Sai dai gwamnatin jihar ta musanta ikirarin nasa.

A watan Janairu ne dai Igboho ya jagoranci matasa wajen lalata dukiya tare da korar Fulani a jihar Oyo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here