Ma’aikatar Mata da Hukumar NAPTIP za su Hada Kai Wajen Yaki da Karuwanci, Safarar Kananan Yara

0
158

Ministar al’amuran mata, Pauline Tallen, ta yi alkawarin hada kai da hukumar hana safara da fataucin kananan yara ta NAPTIP don dakile safarar mutane, Karuwanci da cin zarafin kananan yara a kasarnan.

Bayanin hakan na dauke ne cikin sanarwrar da daraktan yada labarai na hukumar, Shehu Maikai ya fitar a yau Talata.

Maikai ya yi bayanin cewa, Ministar ta yi alkawarin ne yayin da Darakta Janar na Hukumar NAPTIP, Imaan Sulaiman-Ibrahim ya kai ziyarar goyan baya ga ma’aikatar.

Ya ambato ministar na cewa, “Mata da kananan yara sune suka fi samun illa a safarar mutane.

“Idan hukumar NAPTIP da Ma’aikatar Al’amuran mata za su yi aiki tare, dukkansu za su samu nasara wajen magance safarar mata, karuwanci da cin zarafin yara”.

Shugaban hukumar ta NAPTIP ya ce hadin kan zai kasance a fannin samar da aikin yi ga mata da kananan yara;bada horo da ziyarar wayar da kai.

Ministar ta ce: “Zaka yarda dani cewa mafi yawan wadanda ake samu a safarar mutane sune mata da kananan yara.

“Don haka yana da muhimmanci ga hukumar NAPTIP wajen yin aiki da ma’aikatar al’amuran mata domin ta hakan ne zamu samu nasara”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here