Ba za mu amince da kisan Fulani ba a Najeriya -Bashir Tofa

0
222

Sashin Hausa na RFI ya wallafa labarin cewa,  tsohon dan takaran shugabancin kasa a  Najeriya Alhaji Bashir Othman Tofa ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa Fulani makiyaya a kudancin kasarnan wanda ke kai ga rasa rayukansu, yana mai cewa, ba za su amince da haka ba.

A sanarwar da ya raba wa manema labarai wadda Jaridar Daily Nigerian ta wallafa, Tofa ya bayyana kisan a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, wanda ke iya haifar da ramako daga yankin arewacin kasar.

Sanarwar wadda ya yi wa lakabi da ‘Sanarwar Bayyana Matukar Damuwa’ ta ce irin tashin hankalin da suke gani kowacce rana da ya shafi kisan ‘yan arewa a yankin kudu, musamman na Fulani makiyaya a wasu sassan Najeriya abin da ba za a lamunce da shi ba ne.

Tsohon ‘dan takaran shugaban kasar ya ce tabbas akwai yunkurin da wasu makiya daga ciki da wajen Najeriya ke yi na haddasa fitina tsakanin al’ummar Najeriya domin gannin an farraka kasar, kuma jami’an tsaron kasa sun san da su.

Tofa ya ce yau babu wani yanki na Najeriya da ke zaman lafiya, ganin yadda ‘yan ta’adda daga ciki da wajen Najeriya da ke dauke da makamai ke aiki tukuru domin yi wa kasar illa.

Dattijon ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi la’akari da abin da ke faruwa na kashe-kashe da kuma daukar matakan gaggawa domin kawo karshensu.

Tofa ya ce yana kyautata zaton fadar shugaban kasa ta damu da lamarin kuma tana nazari a kansa, amma kuma ya dace a gaggauta daukar mataki a kai.

Tsohon dan takaran ya ce, idan kowanne ‘dan Najeriya ba zai zauna inda yake so cikin ‘yanci da walwala ba domin gudanar da harkokin kasuwancinsa ba tare da ya fuskanci tsangwama ba, to babu wanda za a bari ya zauna a inda ba matsuguninsa ba ne domin gudanar da harkokinsa na yau da kullum.

Tofa ya ce idan an kai wannan mataki, to Najeriya ba ta da kasa na kanta, kuma abin da makiya ke bukata kenan, kuma bai dace akai wannan mataki ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here