2023: Daga Kudancin Najeriya Shugaban Kasa Yakamata ya Fito – Kabiru Gaya

0
82

Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya ya ce daga yankin kudancin Najeriya yakamata ace shugaban kasa na gaba ya fito.

Sanatan wanda ke magana a taron kungiyar NAN a Abuja ranar Talata ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda daga Arewacin Najeriya yake, yana yin abinda yakamata wajen ciyar da kasarnan gaba.

Sannan ya kuma ce, ya aminta cewa shugaban kasa da zai fito nan gaba ya fito daga yankin kudu.

“Kan batun shugabancin kasa a shekarar 2023, zan goyi bayan shugaban kasa daga kudancin kasarnan. Na amince lokaci ne da za mu samu shugaban kasa daga kudancin Najeriya yayin da mataimakin shugaban kasa daga Arewa”, inji shi.

“Ina tunanin zai fi zama adalci a dinga karba-karba a irin wannan yanayin da zai sanya mutane su samu kwarin gwiwa kan lamarin; Arewa da Kudu duk zasu shugabanci juna. Akwai bukatar Najeriya ta zama kasa daya. Hadaddiyar kasa”, inji Sanatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here