Ƙungiyar Izala ta yi Kira ga Gwamnatin Tarayya ta Kara Wayar da Kan Al’umma Kan Allurar Rigakafin Korona

0
151

Shugaban majalisar malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah(JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir , ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su kirkiri karin hanyoyin wayar da kan al’umma kan allurar rigakafin Korona wanda gwamnatin tarayya ke shirin yiwa yan Najeriya.

Sheikh Jingir ya ce yakamata ayiwa yan Najeriya karin bayani kafin a fara amfani da allurar rigakafin.

Malam Jingir wanda shi ne jagoran kungiyar, ya kuma mahukantar kasarnan su tabbatar da ingancin rigakafin yadda baza a sa rayuwar al’umma cikin hadari.

Ya yi kiran ne yayin zantawa da manema labarai a Shelkwatar kungiyar dake birnin Jos.

Sheikh Jingir ya ce, “Gwamnati kar tayi gaggawar karba ko kin karbar allurar rigakafin Korona har sai an tabbatar da ingancinsu da kuma amfaninsu ga rayuwarmu mu al’umma da Allah ya dorawa gwamnati hakkin kula damu.

“Don haka gwamnati kar ra tilasta dokar da zata shafi rayuwar mutum”.

Ya kara da cewa yan Najeriya da dama suna da shakku kan allurar rigakafin don haka kar a tilasta musu yinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here