Korona: An umarci ‘yan sandan Najeriya su tursasa wa mutane sanya takunkumi

0
160

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa,babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya umarci manyan jami’ansa da su tabbatar an tursasa wa ‘yan kasar sanya takunkumi domin kare su daga kamuwa da cutar korona.

Ya bayyana haka ne a sakon da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan kasar Mr Frank Mba ya aike wa manema labarai ranar Litinin.

“Babban Sufeton ‘yan sanda M.A Adamu ya baayr da umarni ga mataimakansa 17 da ke rundunonin ‘yan sanda da ke shiyyoyi da Kwamishinonin ‘yan sanda na jihohi 36 da Abuja, su tursasa bin dokar kare kai daga kamuwa da COVID-19,” a cewar sanarwar.

Ta kara da cewa a yayin da ‘yan sandan za su tabbatar da bin wannan doka, za kuma su yi hakan ne cikin da’a da mutunta jama’ar da ake so a kare su daga kamuwa da cutar.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanya hannu kan umarnin ranar 26 ga watan Janairu yana mai amincewa da daurin wata shida kan duk wanda aka kama ba sanye da takunkumi ba a banar jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here