Gwamnatin Kano ta sanya Masu Larurar Kuturta 526 Cikin shirin Kula da Lafiya Kyauta -Kwamishinan Lafiya

0
138

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta sanya masu larurar kuturta 526 cikin shirin kula da lafiya kyauta a shekarar 2020.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yau Litinin a Kano yayin taron manema labarai kan bikin ranar  kuturta ta duniya da kuma bikin ranar tunawa da cututtukan da ba’a fiye kula dasu ba.

Bikin ranar wadda ake yin ta a duk Lahadin karshen watan Janairu, Majalisar dinkin duniya ce ta sanyata don nuna goyan baya tare da jan hankali kan illar cutar.

Taken bikin na bana shi ne “Kawo karshen Kyama tare da ilmintarwa kan samun lafiyar kwakwalwa”.

Kwamishnan lafiyar, ya kuma ce masu fama da cutar da aka sanya cikin shirin suna daga cikin mutane 4, 734 masu bukata ta musamman, inda ake kula da lafiyarsu kyauta.

Kwamishinan ya kuma bayyana wasu manyan hanyoyin da ake gane cutar ta Kuturta.

Sannan ya yi bayanin cewa, gwamnati ta taka muhimmiyar rawa a fannin rage yaduwar cutukan da ba a kula dasu.

Ya kuma bayyana irin kokarin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na inganta fannin lafiyar jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here