Shin Ƴan Najeriya Zasu Amince da Allurar Rigafin Korona?

0
185

Bayyanar wani bidiyo dake yawo a shafukan sadarwa wanda ke nuna gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello na nun shakku kan ingancin rigakafin Korona ya kara haifar da fargaba tsakanin yan Najeriya.

Duk da gwamnan ya sha musanta cewa akwai cutar Korona, ana ganin kalaman nasa na baya-bayan nan ka iya sa mutanen Najeriya kin aminta da ayi musu rigakafin na Korona.

Kodayake kungiyar gwamnoni ta musanta ikirarin gwmanan na cewa za’a yi amfani da rigakafin ne wajen kashe jama’a inda suka ce su ne sahun farko da za’a fara yiwa allurar ta rigakafin Korona.

A kan hakan ne Jaridar PRIME TIME NEWS ta tattaro ra’ayoyin wasu yan Najeriya kan cewa shin za su yarda ayi musu allurar rigakafin na Korona da zarar ya iso Najeriya?

 

Abubakar Jibril

“Zamu yarda ayi Mana idan mun san mai ta kunsa, ma’ana dame dame aka hadata sannan a bamu dama mushiga laboratory mutantance duk wani abu da take qunshe da shi, sannan mu futo muyiwa jama’a bayani game da amfaninta ka akasinsa wannan shene matsayarmu.”

 

Umar Farouk

“‘Akwai abubuwa masu mahimmanci da suka dace gwamnati ta duba akai wanda suka shafi talaka.

“Ga maleria ita yadace gwamnati ta tsaya tayi duba akansa
Amman saboda basu yake shafaba sunyi burus akansa
Saboda haka su suka san corona kuma su sukeyinta kaga ko su yadace ayiwa wannnan allurar bawai talaka ba.”

 

Jabir Abubakar

“Suzowa kowa da tallafinsa idan suna san mutsaya Amana Allura.Amma akwae raenin wayo ace mana mutsaya A mana allura bayan tallafi sai wanda yayi sa, a yake samu.”

 

Sadiq shehu doguwa (sadiq mai gashi).

“Maganar gaskiya ni dai ban yarda da wannan rigakafin ba, saboda muna ganin irin abubuwan da suke faruwa a duniya.

“Na yarda turawa suke da kai kawo wajen dole sai an kawo wannan allura kasashen africa

“Bayan kuma kowa ya sa ni daga kasahen su wannan cuta ta bullo,

“Sannan mu haryanzu bamu da tabbaci akan wannan cuta ba ina nufin cewa babu ita ba.

“Amma haryanzu idan ka zagaya cikin al’umma idan banda jami’an gwamnati da ake cewa ta kama babu wani ko wata da zai fada maka cewa yasan wani ko wata wacce wannan cuta ta kama.

“To tinda haka ne kaga muna bukatar mugani da idanuwan mu kana musan wasu daga cikin mu wadan da cutar ta kama.

“Idan kuma babu acikin mu to kamata yayi aje wajen wadan da take kamawa sai ayi musu”.

 

Usman Musa Dan Boko.

 

” Bazan Aminta ayimin ba saboda a shekarun baya an yi rigakafi an samu matsala”.

 

Mustapha Sadisu Madugu

“Gaskiya nima ina da shakku kan wannan rigakafin”.

 

Sai dai tuni gwamnonin Arewacin Najeriya suka ce su za’a fara yiwa allurar ta rigakafin domin kau da shakku kan allurar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here