Gwamnonin Arewa za’a fara yiwa Allurar Rigakafin Korona – Simon Lalong

0
96

Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta ce gwamnonin Arewa ne za su kasance mutane na farko da za’a yiwa allurar rigakafin Korona.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya tabbatarwa da manema labarai haka bayan mambobin kungiyar sun amince da shawarar.

“A kokarinmu na kau da shakku kan rigakafin Korona ga mutanen Arewa, kungiyar gwamnonin Arewa ta amince ta kasance sahun mutane na farko da za’ayi rigakafin”, inji gwamnan.

A wani faifan bidiyo dake yaduwa a shafukan sadarwa na zamani, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a Bidiyon na fadin cewa rigakafin koronar zai kashe mutane sai da gwamnonin sun musanta ikirarin nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here