Ganduje Ya Kaddamar Da Dakarun Yaki da Korona Wadanda Za su Tilasta Bin Matakan Kariya daga Cutar

0
137

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya kaddamar da dakarun yakin da Korona 2000 da za su fadakar tare da sanya al’umma su bi ka’idojin kariya daga cutar.

Hakan na cikin kokarin gwamnatin na dakile yaduwar Korona yayin da ake samun yawaitar masu kamuwa da cutar a Kano.

Yayin da yake kaddamar da dakarun na yaki da Korona, Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa baza ta zurawa mutane ido ba suna kin bin ka’idojin kariya daga cutar ta Korona, inda ya kara da cewa dakarun yaki da Koronar za su yi aiki tare da jami’an tsaro don tabbatar da abin matakan kariya daga cutar.

“A yau muna kaddamar da dakarun yaki da Korona a hukumance wadanda za su taimaka mana wajen tabbatar da sun ilimintar da mutane tare da taimakawa wajen hukunra wadanda suka gaza bin matakan kariya daga wannan cutar.

” Cutar Korona ra sake dawo muna zagaye na biyu don haka dole mu dawo da kokarinmu don tabbatar da an dakile wannan annoba.

“Mutane da dama suna mutuwa a wannan lokaci baza mu zura ido mutanen mu su dinga yada wannan cuta ba”.

Ya ce duk da jihar baza ta kara shiga dokar kulle ba, za’a dau matakai don tallafawa wadanda cutar tayiwa illa, inda ya kara da cewa ana tattaunawa da masu ruwa da tsaki don lura da lamarin.
Shima anasa jawabin, shugaban kwamitin kwararru na yaki da cutar ta Korona, Dr. Tijjani Ibrahim, ya bukaci mutane da su tabbata suna bin matakan kariya, inda yayi bayanin cewa zagaye na biyu na cutar yafi hatsari.

Ya ce a duk cikin mutane 100 da ake wa gwajin cutar ana samun mutane 13 dauke da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here