Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta Rufe Gidan Man Aliko tare da cin tararsa Naira Dubu Dari 2

0
372

Gwamantin Jihar Kano ta ci tarar gidan man Aliko da ke Dakata a karamar hukumar Nasarawa ta Kano Naira dubu dari biyu tare da rufe shi nan take sakamakon karya dokar tsafatar muhalli.

Haka kuma an rufe tashar motoci ta Kano Line bisa rashin bin dokar tsaftar Muhalli ta karshen wata.

Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin rangadin duba yadda ake gudanar da tsaftar muhallin a Jihar Kano.

 

Akwai karin bayani nan gaba……

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here