Shugabar Ƴan Jaridu Ta Mutu Kwana Biyu Bayan ta Haifi Ƴan Tagwaye

0
220

Shugabar kungiyar yan Jarida ta Najeriya, reshen jihar Benue, Comrade Victor Asher ta mutu.

A wata sanarwa da sakataren kungiyar yan jaridun na jihar Moses Akarhan ya fitar ta ce, Asher ta mutu a yau Asabar da karfe 8 na safe a babban Asibitin tarayya dake Makurdi bayan yi mata aiki.

Sakataren ya kuma yi bayanin cewa, kungiyar za ta sanar taron zabe na gaggawa don maye gurbinta.

Marigayi Asher ta haifi yan tagwaye biyu- mace daya namiji daya a ranar 23 ga watan Janairu kafin rashin lafiyarta tayi tsamari.

Ta zama shugabar kungiyar yan Jaridu a jihar Benue ne a watan Disamba na shekarar 2018 bayan rasuwar wanda ta gada, David Ukuma, wanda ya zama shugaban kungiyar a 3 ga watan Yuli kafin rasuwarsa.

Kafin rasuwar Asher, tana aiki da gidan Rediyon jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here