Masu Amfani da Layukan Airtel Miliyan 23 ne Basu Tura Lambar NIN din su Ba yayin da ake shirin rufe layukan a Fabarairu

0
100

Adadin masu amfani da layin waya na kamfanin Airtel Miliyan 23.4 ne har yanzu basu tura lambar katin shedar dan kasa don hada su da lambobinsu kamar yadda kididdigar da kamfanin ya fitar ta nuna.

Shugaban Kamfanin Airtel yankin Afrika, Raghunath Mandava ne ya fitar da kididdigar a wani taro da aka yi jiya Juma’a.

Ya ce Kamfanin Airtel ya karbi lambar katin shedar dan kasa ta mutane miliyan 21 cikin mutane Miliyan 44.4 dake Amfani da layin, inda mutane miliyan 23.4 suka gaza tura lambobin inda hakan zai sa a toshe layukansu.

Ya ce kamfanin layin wayar na Airtel yana aiki don inganta alaka da hukumar dake bayar da katin shedar zama dan kasa wajen tantance lambabin.

“Mun samar da hanya mai kyau ta daukar lambar NIN tare da shirya bayanai da hukumar NIMC. Cikin Masu amfani da Layin Airtel Miliyan 44.4, mun karbi lambar NIN ta mutane miliyan 21 wato kashi 47”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here