Shugaban Kasa Buhari Ya tafi Garin Daura Don Yin Rijistar Zama Dan Jam’iyyar APC

0
164

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar birnin Abuja zuwa Daura ta jihar Katsina, don yin rijistar shedar zama dan jam’iyyar APC.

Shugaban kasar ya bar Abuja ne jim kadan bayan ya idar da Sallar Juma’a a masallacin fadar shugaban kasa.

Tun da farko dai sai da shugaban kasar ya karbi bakuncin gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong wanda ya bayyanawa manema labarai na fadar shugaban kasa cewa, ya gana da shugaba Buhari ne don yi masa bayani kan batutuwan da suka shafi tsaro.

Yayin da ya isa garin Daura, Shugaba Buhari zai yankin katin shedar zama dan jam’iyyar APC da misalin karfe 12 na rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here