Korona: Gwamnatin Najeriya Na Shirin Sanya Dokar Kulle a Abuja da Legas

0
126

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar korona na duba yiwuwar sanya dokar kulle a babban birnin tarayya Abuja da Legas da Plateau.

Ɗaya daga cikin jami’an kwamitin, Mukhtar Muhammed ya tabbatar da hakan a yau Juma’a yana mai cewa karuwar masu dauke da annobar akwai damuwa sosai musamman a biranen wadanan jihohi 2 da Abuja.

Alkaluman hukumar daƙile cutuka masu yaduwa wato NCDC ya nuna cewa cutar tafi yawa a Legas inda mutum 46,935 ke dauke da cutar, sannan Abuja mai mutum 16,470, Plateau ke mataki na uku da mutum 7,801.

Har yanzu dai sabbin alkaluma na sake bayyana, kuma masu mutuwa na ƙaruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here