RAHOTO NA MUSAMMAN: Menene Makomar Yakubu Dogara a APC da PDP ?

0
114

…….Jam’iyyar APC ta ce Babu Sunan Dogara Ckin Rijistar Sunayen Mambobinta Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

……….Kakakin Majalisar Wakilai bai bayyana sauya shekar Dogara a Majalisa ba.

Tun bayan bullar labarin sauya sheka da tsohon kakakin majalisar Wakilan Najeriya, Yakubu Dogara ya yi a watan Yuni na shekarar bara, aka samu rashin jituwa a jam’iyyar PDP da kuma jam’iyyar da ya koma wato APC.

Hakan ya samo asali ne daga lamarin da ya kai ga Yakubu Dogara ya fice daga PDP zuwa APC.

Abubuwan da suka faru a yan kwanakin nan yayin da yake rike shedar dan jam’iyya biyu ya haifar da hasashe da dama inda aka rasa ina ne makomarsa.

Duk da shugaban riko na Jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni ya tabbatar da sauya shekarar ta Yakubu Dogara bayan ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma ba a sanar da sauya shekar ta Yakubu Dogara ba a zauran majalisar Wakilan Najeriya kamar yadda aka sanar da sauya shekar wasu yan majalisar da suka koma APC daga APGA da PDP.

Tsohon kakakin majalisar Wakilan wanda ke wakiltar kananan hukumomon Dass/Bagoro/Tafawa Balewa ya fice daga Jam’iyyar APC zuwa PDP a zaben shekarar 2019.

Dogara wanda yake cikin yan gaba-gaba na yaki don rusa APC ya bar jam’iyyar bisa rashin jituwarsu da gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar a lokacin.

Rikicin siyasa dake tsakanin sa da tsohon gwamna Mohammed Abubakar ne ya haifar da samun nasarar Sanata Bala Mohammed na PDP.

Kodayake, tsohon kakakin majalisar ya kuma samun sabani da gwamna Bala Mohammed wanda hakan yasa shi barin PDP da sake komawa APC.

Jaridar ta Daily Trust ta rawaito cewa, yayin zaman Kotu don sauraron karar da PDP ta shigar tana kalubalantar komawar Dogara APC a Abuja, Jam’iyyar APC a martanin da ta mayar ta ce babu sunan Dogara a rijistar mambobinta.

A bayanan da jam’iyyar ta shigarwa da Kotu mai dauke da sa hannun shugaban sashin kula da shari’a na APC, Dare Oketade ya yi ikirarin cewa bashi da masaniya kan sauya shekar da Yakubu Dogara ya yi daga PDP kuma bai ga sunansa ba a rijistar mambobin jam’iyyar.

A kara mai Lamba FHC/ABJ/CS/1060/2020 da mambobin jam’iyyar PDP na Bauchi suka shigar ta hannun lauyansu, Jibrin S Jibrin, suna sukar sauya shekar da Yakubu Dogara ya yi zuwa APC.

Wadanda ake karar dai sun hada da; Dogara, Kakakin majalisar wakilai, Antoni janar na kasa, hukumar zabe ta INEC da jam’iyyar APC.

Jam’iyyar PDP da shugabanta na Bauchi Hamza Koshe Akuyam sun yi bayanin cewa Dogara ya samu nasara lashe zabe a jam’iyyar ta PDP.

Jam’iyyar ta ce Dogara ya watsar da PDP yayin da ya mika wasikarsa ta barin jam’iyyar ga shugabanta na Mazabar Bogoro C a ranar 24 ga watan Yuli na shekarar 2020.

Jami’iyyar ta kafa hujja da sashi na 68(1)(g) na kundin tsarin mulkin Najeriya wnada ya yi bayanin cewa, Dogara zai bar kujerararsa bisa fice daga PDP, jam’iyyar da ya samu nasarar lashe zabe a ciki.

Shugaban jam’iyyar ta PDP a Bauchi ya ce babu wani rikici a jam’iyyar ko rabuwar kai wanda zai sa Dogara ya bar jam’iyyar.

Sai dai har yanzu ba’a sanar da sauya shekarar Yakubu Dogara a majalisar wakilai ba.

Kamar yadda aka saba ana sanar da sauya shekar wani mamba na majalisar a zauren majalisar.

Kodayake, watanni bayan sauyin sheka da Yakubu Dogara ya yi , har yanzu kakakin majalisar wakilan bai sanar da sauya shekarar tasa ba.

Kuma, Yakubu Dogara ya ja bakinsa ya yi shiru kan batun sannan baya shiga al’amuran majalisar tun lokacin da ya bar shugabancin majalisar.

Yayin tattaunawar da Jaridar Daily Trust ta yi da wani jigo a APC a Bogoro ya ce bashi da tabbas ko an bawa Yakubu Dogara katin shedar zama dan jam’iyyar a mazabarsa.

Wani Jigo a jam’iyyar dake jihar ya shaidawa jaridar cewa Dogara mamba ne na APC, sannan ya musanta jita-jitar da ake yadawa kan batun makomar Dogara.

Hakan ya haifar da dar-dar kan makomar Dogara yayin da mutane ke bayyana ra’ayinsu kan yadda kowanne bangare na PDP da APC ke nuna baya tare da Dogara.

Zuwa yanzu dai, sanarwa ko karin bayani daga wadannan jam’iyyu ko kuma hukuncin koto ne zai fayyace makomar Yakubu Dogara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here