NANS ta Goyi Bayan Tsarin yiwa Ɗalibai Gwajin Shan Miyagun Kwayoyi Kafin a Basu Gurbin Karatu a Jami’o’i

0
268

Kungiyar Dalibai ta kasa(NANS) ta goyi bayan shawarar hukumar dake yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA na yin gwajin shan miyagun kwayoyi ga daliban da ke son shiga manyan makarantu.

Shugaban kungiyar ta NANS, Kwamaret Asefon Daye ne ya bayyana goyan bayansa kan shawarar yayin da ya kai ziyarar nuna goyan baya ga shugaban hukumar NDLEA, Janar Buba Marwa mai ritaya a Abuja ranar Laraba.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da babban jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA, Jonah Achema ya fitar.

Sanarwar ta rawaito Daye na cewa, shan miyagun kwayoyi ya jawo illa sosai ga Daliban Najeriya.

“Muna Goyan bayan tsarin yin gwajin shan miyagun kwayoyi. Kwayoyi sun yi illa sosai ga daliban Najeriya. Bama son daliban Najeriya su ci gaba da mutuwa sabida shan kwaya”, inji shi.

Shugaban na NANS ya ce tsarin yin gwajin shan miyagun kwayoyin ba wai zai zama kariya kadai ba zai karfafa gwiwar masu yi kan su dena dabi’ar ta shan miyagun kwayoyi.

Shugaban hukunar ta NDLEA ya yabawa kungiyar daliban bisa ziyara da suka kawo masa tare da nuna goyan baya ga hukumar.

Sannan ya yi kira gare su da su kafa kungiyoyin yaki da shan miyagun kwayoyi a makarantu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here