Bidiyon Dala: Ganduje Na Son Kotu ta bashi Damar Gyara Shaidu da Bayanai

0
223

Babbar Kotun jihar Kano ta sanya ranar 8 ga watan Mayu na shekarar 2021, don yin hukunci kan bukatar gyara sunayen shaida da za’a kirawo a shari’ar dake gudana tsakanin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Dan Jarida, Jafar Jafar.

Gwamna Ganduje ya shigar da karar Jafar Jafar gaban kotun bisa wani faifan Bidiyo da jaridar Daily Nigerian ta fitar wanda ke nuna gwamanan na cusa Dala a aljihun babbar riga wanda ake zargin toshiyar baki ne daga yan kwangila.

Ganduje ta hanyar lauyansa ya gabatar da bukatar a ranar 10 ga watan Nuwamba na shekarar 2020 inda yake neman kotun ta bashi damar gabatar da karin bayanaai na sheda.

A zaman kotun na yau Alhmis, lauyan Jafar Jafar, UU Etem, ya soki bukatar ta Ganduje inda ya ce ya saba da ka’idar shari’ar da kotun ke yi.

Kodayake, Lauyan Ganduje, MN Duru ya jaddada cewa bukatar na kan ka’ida.

Mai shari’a Sulaiman Baba Namalam, ya dage sauraron karar zuwa 8 ga watan Mayu don yanke hukunci tare da ci gaba da sauraron karar.

Idan za’a iya tunawa dai, a wani faifan bidiyo da aka fitar, an ga gwamna Ganduje na karbar toshiyar baki na daloli da yawansu ya kai Dala miliyan 5.

Sai dai gwamnatin Kano ta musanta batun inda ta shigar kamfanin jaridar tare da mawallafinta kara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here