Akwai Bukatar Najeriya ta Fara Shirin Tunkarar Annobar da za ta zo nan Gaba – Bill Gates

0
141

Bill Gates, shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates ya ce akwai bukatar gwamnatoci a fadin duniya ciki har da Najeriya su fara shirin tunkarar wata annoba a nan gaba.

Yayin da yake amsa tambayar jaridar TheCable, Bill Gates ya ce kasashe kamar Najeriya akwai bukatar su kara sanya kudade a fannin lafiya matakin farko don tabbatar da an shirya tunkarar annobar duniya da za ta zo nan gaba.

Attajirin kasar Amurkan ya ce yan Najeriya da dama suna mutuwa duk shekara daga matsalolin kula da lafiya matakin farko fiye da yadda Korona ta kashe mutane a Afrika.

“Ina nufin mace-macen da ake samu daga matsalolin fannin lafiya matakin farko na karuwa duk shekara fiye da yadda annobar Korona ke kashe mutane a Afrika, ina fatan hakan zai sa kowa ya lura da wannan kalubale”, ini Bill Gates.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here