An Samu Ɓullar Sabon Nau’in Annobar Korona ta Burtaniya a Najeriya

0
182

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, shugaban hukumar daƙile cutuka masu yaduwa ta NCDC a Najeriya, Dr Chikwe Ihekweazu ya shaida cewa an samu ƴan ƙasar hudu dauke da sabon nau’in annobar korona mai haɗari irin ta Burtaniya.

Ihekweazu, ya ce daga cikin wadanda aka samu dauke da cutar uku ƴan ƙasar ne da suka dawo daga balaguro, sai kuma ɗaya da bai je ko ina ba.

Ya shaida cewa ba abin mamaki bane samun bullar wannan nau’in a ƙasar la’akari da yada ake tafiye-tafiye tsakanin Burtaniya da Najeriya.

NCDC ta ce zata cigaba da daukan matakai da fadada ayyukanta da hadin-gwiwar da take samu, ganin cewa rufe ko hana jiragen ƙetare sauka a ƙasar a yanzu da wuya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here