Ƙungiyar Ɗalibai ta Gwale ta Kafa Kwamitin Riƙon Ƙwarya

0
193

Bayan shafe a ƙalla shekaru sama da biyar kungiyar Dalibai ta karamar hukumar Gwale wato GWALSU, ba ta motsi, a karshen Makon da ya gabata wasu daga cikin daliban karamar hukumar daga makarantu daban daban da kuma masu ruwa da tsaki na kungiyar suka samar da shugabancin riƙon ƙwarya wadda kuma suka kaddamar da shi.

A yayin taron ne aka zabi Comrade Zakariyya Jafar Muhammad Galadanchi a matsayin shugaban kwamitin  riƙon ƙwarya na kungiyar, kuma daga cikin ayyukan da aka Dorawa kwamitin sun haɗar da:

Bin dukkan makarantu tare da samar da wakilai na musamman wadanda zasu yi aiki tare, makarantun kuma sun haɗar Jami’ar Bayero Kano, Kwalejin Fasaha, Jami’ar kimiyya da fasaha ta garin Wudil, Kwalejin Sa’adatu Rimi, Kwalejin Legal da sauran su.

Samar da Kundin bayanai dake dauke da bayanan daliban su makarantu da wakilan suka fito domin shiryawa babban zaben Ƙungiyar na Matakin karamar hukumar baki daya.

Samar da shugabanni na musamman wadanda zasu shirya zaɓen da kuma gudanar da shi daga makarantu daban daban.

Kiran babban taro tare da bayar da bayanan da shugabannin Riƙon kwarya suka tattara domin tunkarar babban zaben.

Da yake zantawa da Jaridar PRIME TIME NEWS,  sabon shugaban Ƙungiyar na riƙon ƙwarya Comrade Zakariyya Galadanchi ya tabbatar da cewa zasu yi aiki Tukuru wajen sauke nauyin da aka rataya musu akan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here