Yan Sanda sun samu Nasarar Cafke miyagun barayin da suka Addabi Al’umma a jahar Yobe

0
112

 

DAGA Abdulrashid Abdullahi,Kano

Jami’an rundunar ‘yan sanda na “OPERATION HABA MAZA ” dake garin Damaturu sunyi nasarar cafke wasu matasa barayi da suka addabi Al’umma a garin Damaturu, musamman unguwannin yan’ya, Obasanjo, 3bed Room, malari, dakuma Estate.

Barayin wanda aka samu nasarar cafke su cikin dare da misalin karfe 2, na dare , sun bayyana da kansu cewa mafi yawansu ba Yan jahar Yobe, bane daga wasu garuruwa suke zuwa garin Damaturu don gudanar da mummunan aikin nasu.

Sun shahara wajen kwacen waya, shiga gidajen mutane da makamai da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here