Jami’ar Legas za ta Gudanar da Jarrabawar Post-UTME ta Kafar Sadarwa

0
131

Shugaban jami’ar jihar Lagos, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, ya bukaci mawadatan Najeriya su tallafawa daliban dake neman gurbin karatu a jami’ar don su samu na’urar Tablet, yayin da jami’ar ta shirya gudanar da jarrabawar Post-UTME ta kafar sadarwa.

Ogundipe ya yi kiran ne yayin tattaunawa da kamfanin dillacin labarai na kasa(NAN) yau Lahadi a birnin Lagos..

Ya ce bisa bullar annobar Korona, dukkan harkokin karatu na jami’ar da suka hada da jarrabawa za’a yi su ne ta kafar sadarwa.

“Zamu gudanar da jarrabawar Post-UTME ranar 15 ga watan Fabarairu zuwa 23; za’a shafe ranaku 9 ana yin jarrabawar.

“Jarrabawar za ta gudana ne ta kafar sadarwa, a duk inda dalibi yake babu bukatar yazo makaranta. tana da sauki kuma da gamsarwa.

“Yanzu mun fara tattaunawa da abokan wannan jami’a da kungiyoyin tsofaffin dalibai don ganin yadda zamu samu na’urar da zamu rabawa masu neman gurbin karatu”.

Ya ce sama da mutane dubu 50 ne suka nemi jami’ar a shekarar karatu ta 2020/2021, yayin da 22, 000 suka samu maki 200 zuwa sama a jarrabawar Jamb.

Sannan dalibai 21, 955 ne suka biya kudin zana jarrabawar ta Post-UTME.

“Wannan ne karo na farko da zamu gudanar da irin wannan jarrabawar, kuma dole ne masu zana jarrabawar su samu na’urar mai kwakwalwa dake da na’urar daukar hoto.

” Muna tsammanin sakin sakamakon jarrabawar cikin mako guda, “inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here