Zamu Samar Da Dakarun Yaki da Cutar Korona a Kano – Ganduje

0
61

Gwammatin Kano na shirin samar da Dakarun Korona wadanda za su tilasta bin ka’idojin kariya daga cutar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da hakan a yau Asabar yayin da yake taro da yan Jarida a gidan gwamnatin Kano.

Ya ce akwai bukatar a dakile yaduwar cutar Korona da dukkan matakan da suka dace, inda ya yi bayanin cewa rashin bin ka’idojin kariya daga cutar ne babban kalubale na hana yaduwar cutar.

Ganduje ya ce, gwamnatin jihar ta tattauna da duk hukumomin dake da ruwa da tsaki don nemo hanyar yadda za’a tabbatar da anbi ka’idojin.

“Kwanan nan za’a tilasta bin ka’idojin kariya daga cutar Korona a wannan jihar. Mutane yakamata su bi ka’idojin don kare lafiyar al’umma.

“Kwamitin kar ta kwana na yaki da Korona ya zauna tattaunawa da jami’an tsaro don fara sanya al’umma su bi ka’idojin kariya daga cutar Korona”, inji shi.

Gwamnan ya ce dakarun yaki da Koronan za su hada da jami’an tsaro da kungiyoyin masu zaman kansu.

Sannan yayi kira ga kafafen yada labarai kan su ci gaba da wayar da kan al’umma hadarin annobar.

“Muna matukar farin ciki yadda kuke bawa gwamnatin jiha hadin kai a wannan yakin”, inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here