Zagin Malamai Da Rashin Biyayya Ga Iyaye shi Ya Tarwatsa Arewa

0
153

 

Daga Mukhtar Sagir Dambatta
21/01/2021

Hakika Arewa muna cikin wani hali na rashin tsaro, talauci, da kuma rashin aikin yi kuma a haka mutane suke ta neman mafita ta kowacce irin hanya.

Malamai suna da matukar tasiri a rayuwar kowacce alumma musamman a bangaren tarbiyya da kuma ilimi na zamantakewar yau da gobe. Mutane suna zagin malamai suna muzan tasu suna jifan su da kalamai marar sa dadi wanda duk wanda aka yiwa haka a karan kansa ba zai ji dadi ba.

Mutane sun manta cewa kowacce irin masifa da annoba maganinta addu’a ba wai zagin malamai ba. Sai kaga mutum ko Alqur’ani da hadisi bai sani ba amma yana budar baki yana cewa malami jahili ko kuma mahaukaci, Ya kamata mutane su sani cewa koda malami yayi ba dai dai ba addu’a ya kamata a yi masa ba wai zagi ba.

Rashin biyayya ga iyaye da kuma na gaba na cikin dalilan da suka kawo mana koma baya a cikin rayuwar mu. Zaka ga mutum iyayensa na masa magana amma yana amsa musu kamar shi ya haifesu, Zaka ga mutum yayansa ko wani wanda ya girme shi yana masa magana amma sai yayi kamar bai jiba. Kaji mutum yana fadawa iyayensa magana yanda yaga dama ba tare da nuna biyayya da kuma risinawa ba.

Allah yana sanya wa mutumin da yake girmama malamansa da kuma iyayensa albarka. Wannan yanki namu yana cikin wani hali na tausayawa amma iyaye da yayye sun koma gefe sun zuba ido domin yayansu da kannansu basa musu biyayya

Tabbas mutum zai samu daukaka idan ya kasance iyaye da malamai na masa addu’ar fatan alkhairi a kowanne bangare. Bin iyaye da sanin darajar malaman ka shine zai sanya maka farin ciki a koda yaushe

Idan muna san chigaba da zaman lafiya a wannan yanki dole sai mun daina zagin malamai kuma mun koma girmama iyaye da kuma na gaba da mu

Allah ya albarkace mu da malamai masu ilimi da hazaka amma kullum cikin zagin su ake ana musu fatan tsiya. Iyaye kuma ana musu kallan marar sa daraja.

Allah ya sa mu gyara. Allah ya albarkaci iyayen mu da malaman mu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here