Hukumar KAROTA ta Kano ta Cafke wata mota Kirar Golf Cike da tabar WiWi

0
178

 

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Hukumar Karota, Mai kula da zirga-zirgar Abubuwan hawa a jahar Kano, Karkashin jagorancin Shugabanta Dakta Bappah Babbba Dan Agundi,tayi Nasarar cafke wata mota taksi Kirar “Golf” makare da tabar WiWi aciki.

An Kama manyan Buhunhuna guda uku, Kimanin Pieces 178 a daidai kofar Kansakali zuwa kofar Dawanau a tsakar daren ranar talatar da ta gabata.

Tuni dai Shugaban Hukumar ta Karota ya bada umarnin a mika motar da kayan a hannun Hukumar hana Sha da fataucin miyagun kwayoyi reshan jihar Kano wato NDLEA Dan daukar mataki na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here