2023: ‘Wallahi Buhari Ba zai Goyi Bayan Takarar Bola Tinubu ba’ – Sule Lamido

0
113

Tsohon gwamman jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bazai taba goyan baya takarar jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu ba.

Sai dai har yanzu Bola Tinubu bai bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban kasa ba a shekerar 2023.

Sai dai yayin da yake jawabi a taron kaddamar da Kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP na Jihar Jigawa a yau Laraba.

Ya ce jam’iyyar ta APC ta gida biyu ce wato Buhari da Tinubu.

Ya ce: “Jam’iyyar APC ta mutane biyu ce, Buhari da Tinubu kuma ina fada muku Wallahi! Wallahi! Wallahi!, Buhari bazai goyi bayan Tinubu ba a zaben gaba”.

Tsohon ministan ya ce, Buhari ya cika burinsa na yin mulki zango biyu ba tare da samun nasarar manufofinsa guda uku ba ba wato Magance matsalar tsaro, yaki da cin hanci da rashawa da bunkasa tattalin arziki.

Sule Lamido ya yi ikirarin cewa, Buhari ya yaudari yan Najeriya kamar yadda Donal Trump ya yaudari kasar Amurka.

Haka kuma ya kalubalanci mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana wadanda jam’iyyar APC ta fitar da ga talauci a jihar Jigawa.

“Ina Kalubalantar bayanan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na fitar da mutane miliyan 20 daga talauci. Muna so musan wadanda aka fitar daga talauci a jihar Jigawa”, inji Sule Lamido.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here