Ƴan sanda sun Cafke Ɗaya daga cikin Ma’aikatan jami’ar A.B.U Zariya, da yake Temakawa masu Garkuwa da mutane

0
181

 

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Rundunar Yan sanda tayi holen wani mutumi Mai suna Ja’afaru, Wanda ma’aikacine na tsaro a jami’ar Ahmadu Bello university, dake zariya.

Mutumin da aka Cafke ana zarginsa da temakawa masu Garkuwa da mutane da suka sace wasu daga cikin malamai da dalibai na Makarantar A kwanakin baya.

Mai magana da yawun Rundunar Yan Sanda na Kasa Mr. Frank Mba, yace jamian Rundunar Yan Sanda ne sukayi nasarar kamo mutumin da ake zargi Yana hulda da masu Garkuwa da mutane Wanda ya Basu bayanin wani malamin jami’ar da akayi Garkuwa dashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here