Gwawmnatin Kano ta ce Bata da niyyar siyar da Gidan marayu na Nassarawa

0
103

 

Gwawmnatin Jahar Kano ta ce Bata da niyyar sayar da Gidan marayu na nassarawa, Koh sauyawa wa marayun Guri.

Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata da Walwalar jama’a ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad Umar, ce ta bayyana hakan a harabar ofishinta dake Ma’aikatar.

Dakta Zahra’u ta bayyana cewa Ma’aikatar ce ta ga ya dace ta dauki wasu daga cikin marayun daga Nassarawa, zuwa Cibiyar Gaya a Matsayin gwaji,saboda Kar abar wajen ba kowa ya lalace.

Kwamishiniyar ta nanata cewa jama,a suyi watsi da duk wata jita jita da ke yawo a Gari cewa gwamnati ta dauki aniyar sayarda gidan yaran Na Nasarawa.

Dakta Zahra,u tace gidan Marayu na Nasarawa shima zaman kansa yake yi wani Kari ne aka samu domin Al’ummar sake garin Gaya da kewaye su amfana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here