Ganduje na Son Aikin Janyo Gas Ya Fara Daga Kano Zuwa Kaduna

0
116

 

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ba da shawarar cewa aikin janyo Gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano ya kamata ya fara ne daga jahar Kano, ta yadda zai tafi zuwa ga kaduna, ba daga Kaduna zuwa Kano ba.

Ya bayyana hakane , a taron wayar da kan jama’a kan ayyukan yi na jihar Kano, wanda aka yi a gidan gwamnatin Kano, ranar Litinin, yaci gabada cewa, ta wannan hanyar ne za a aiwatar da aikin ne Kano za ta sake jin daɗin wannan kyakkyawan matakin.

An tsara taron ne don masu ruwa da tsaki tare da manufar fadakarwa da sauƙaƙe manufar sauya kamfanoni daban-daban waɗanda cutar ta COVID-19 ta shafa. Hakan ya haifar da babbar illa ga ci gaban tattalin arzikin jihar da kasa da duniya baki daya.

“Muna son wannan aikin iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano ya fara daga Kano zuwa Kaduna. Sannan kuma ya taho daga Ajaokuta zuwa Kaduna, ita ma. Daga nan sai mu hadu a tsakiyarta duka,” in ji shi.

Yin he aikin iskar gas na nufin ci gaba mai mahimmancin gaske ga jihar Kano inda masana’antu za su farfaɗo, tare da ayyukan yi ba tsayawa.

“Da wannan za mu iya tabbatar da cimma nasarori da yawa. Saboda da gas, masana’antunmu za su samar da kaya cikin rahusa sabanin amfani da wutar lantarki.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here