Ba da Son Ranmu a Ka Koma Makarantu ba, Zamu sake yin Nazarin ranar Komawa Makarantun – Ministan Ilimi

0
174

Gwamnatin tarayya a jiya Litinin ta ce ba ta goyan bayan komawa makarantu a ranar 18 ga watan Janairu kuma za ta sake yin nazari kan ranar komawa makarantun.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, a yayin taron jawabi da kwamitin yaki da Korona ke yi a Abuja ya ce gwamnatin tarayya ba ta amince da jihohi ba kan ranar komawa makarantun.

Adamu Adamu, wanda yayi bayanin cewa kwamitin zai duba yanayin yadda annobar Korona take a kullum, sannan za’a sake yin nazari na ranar komawa makarantu.

“Mun zauna, mun lura da yadda ake samun adadi mai yawa na masu kamuwa da cutar Korona kuma mun amince cewa baza a bude makarantu ba.”

Idan za’a iya tunawa dai a ranar Alhamis da ta gabata, a wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta tarayya, Ben Goong ya fitar ta ce, ” bayan tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnonin jihohi, kwamishinonin ilimi masu makarantu da shugabbanin makarantu an amince da komawa makarantu ranar 18 fa watan Janairu”.

Shima anasa jawabin, Sakataren gwamnatin tarayya, kuma shugaban kwamitin yaki da Korona, Boss Mustapha ya ce za’a sake yin Nazari kan ranar komawa makarantun sakamakon yawaitar samun masu kamuwa da cutar Korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here