An yi Kira ga Masu Hannu da Shuni da Su dinga Tallafawa Marayu da Masu Karamin Karfi

1
113

Daga Abdulwahab Edrees Suleiman.

Babban Limanin Masallacin Kasa dake Abuja farfesa, Ibrahim Makari,  ya yi Kira ga masu hannu da shuni da su dinga taimakawa marayu Wadanda iyayensu suka rasu suka barsu.

Farfesa Makari,  ya yi Wannan Kiran ne a wani taron Maulidi da aka gabatar a unguwar Bachirawa ta karamar hukumar Ungogo dake jihar Kano inda taron Maulidin ya samu halartar manya manyan Malamai da sha’irai hadi da manyan Yan kasuwa na cikin Kano da wajenta, Bugu da Kari  taron Maulidin ya sa mu halartar Mataimakin Gwamnan Jahar Kano Dr. Nasiru Yusif Gawuna.

Farfesa Makari,  ya ce “tun a lokutan baya yaso ace yana Daya daga cikin kwamitin shirya Wannan Maulidi inda kamar yanda kowa yasan ana Maulidin nan a Wannan unguwa Haka zai qara tabbatarwa sabo kamar yanda duk wani mahalarcin Maulidin nan yasan ana bayar da kyautar kujerar umara da motoce to Haka zai qara tabbatar ne da yanxu abun ya sauya”.

Ya ce “idan za’a duba Wannan unguwar ba za’a rasa marayu ba wanda iyayensu suka mutu suka barsu,Wanda Kuma yanxu wasun su basa zuwa makaranta,da Kuma marasa lafiya Wanda suke kwance gadon Asibiti.”

Bayan ya bayyana hakane sai suma kwamitin Maulidin su kace hakan yayi Kuma tun agun kasa samu gudunmawar million 1 Domin Fara Wannan abun alkhairi tun a Wannan lokacin kafinma shekara me zuwan din.

Shi ma anasa jawabin Jagoran kungiyar Jama’atu Ahababu Rasulullah Assocition of Nigeria, Shekh Sharif Sani Janbulo ya yi kira ga al’ummar musulmi da su dinga koyi da irin halayen Manzon Allah S.A.W.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here