Majalissar wakilai ta bukaci a Dage lokacin sake bude makarantun kasarnan zuwa watanni 3 masu zuwa

0
170

Daga Abdurashid Abdullahi

Majalissar wakilai ta nijeriya, ta kalubalanci umarnin da gwamnatin Tarayya ta bayar na sake bude makarantun a Gobe Litinin saboda karuwar yawan Mutanen da suke harbuwa da Annobar sarkewar numfashi ta Covid 19.

Shugaban kwamitin Ilimi na Majalissar Farfesa Julius Ihonvbere, cikin wata sanarwa da aka fitar, yace gwamnati bata tuntubi majalissar wakilai ba, sabanin Ikirarin da akeyi cewa an tuntubi dukannin masu ruwa da tsaki kafin bude Makarantun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here